8

Me Ya sa Thomas Harvey ya sace kwakwalwar Albert Einstein?

Thomas Harvey rike da kwakwalwar Albert Einstein
Dr. Thomas Harvey rike da kwakwalwar Albert Einstein a cikin gilashi

A kimiyyance da likitanci na zamani akwai wasu irin likitoci da aikinsu shine gano musabbabin mutuwar mutum bayan yin wasu gwaje-gwaje a gawarsa, wadannan masana kimiyya ana kiransu da “autopsists”, kuma “forensic pathologists” Sannan akwai wasu kuma wadanda suka kware a kan karantar cuta da musabbabinta, hatsarinta da yadda take wanzuwa ko da ace ta kasance sabuwa ce, su ma wadannan likitoci ana kiransu da “pathologists”, kamar yadda Dr. Thomas Harvey ma ya kasance kwararre daga cikinsu.

masani albert einsten
Masanin kimiyya Albert Einstein

A nanar 18th ga watan April na shekarar 1955 shahararren masanin kimiyyar nan Albert Einstein ya mutu a kasar Amurka bayan ya shafe wani lokaci yana fama da rashin lafiya. Einstein ya mutu yanada shekaru 76 a duniya, kamar yadda magajinshi a kimiyyance masani Stephen Hawking ya mutu a shakarar 2018 bayan ya shafe shekaru 76 cif yana rayuwa a wannan duniyar. Hakika wannan abu yayi matukar ba wa mutane mamaki ganin yadda wadannan mutane suka rayu a daular kimiyya kuma suka ba wa duniya gudunmawa a fanni iri daya, kuma suka mutu yayinda suka kai shekaru iri daya.

Fikirar wannan babban masani Albert Einstein ta shahara a duniya matuka a inda ya kasance na daban wajen tunani wa warware wata matsalar kimiyya. Einstein ya bada gudummawa a duniyar kimiyya sosai, a inda ya zama masanin kimiyya mafi shahara a karni na 20. Fikirar Einstein ta kai da cewa ko da ana son danganta wani da wata baiwa ta musamman a makaranta to sai ayi masa lakabi da “Einstein” a inda Kalmar ta maye gurbin kalmomin “gifted” ko “genius”

Kadan daga cikin gudummawar da Einstein ba wa duniyar sun hada da kirkirar nazariyyar relativity (special theory of relativity da general theory of relativity), photoelectric effect, black hole, quantum theory, photon da sauransu. Akwai littatafansa da suka hada da The World as I see It, The Evolution of Physics, Ideas and Opinions da sauransu.

A lokacin da wannan masani ya mutu a kasar Amurka sai aka kira Dr. Thomas Harvey domin yin binciken kwakwaf kan gano musabbabin mutuwarsa. Ganin wannan dama ta kasancewarsa shi kadai (daga shi sai gawar Einstein) a wannan dakin bincike na asibitin, sai Dr. Harvey yayi amfani da wannan damar ya fasa kan Einstein ya zare kwakwalwarsa ya boye, sa’annan ya dinke kan ya mayar da komai yadda yake ya ci gaba da gudanar da bincikensa. Bayan ya gama ne ya sanar da mahukunta sakamakon bincikensa kan matakin da za su dauka akan wannan gawa.

Daman Einstein kafin ya mutu ya bayar da wasiyyar cewa idan ya mutu a kona gawarsa wato “cremation” a turance kamar yadda ma’abota addinin Hindu suke yi.

Bayan duk wadannan abubuwa da suka faru, Dr. Harvey bai sanar da mahukunta game da sace kwakwalwar Einstein da yayi ba, sai zuwa yayi dakin binciken kimiyyarsa ya adana ta yadda ba za ta rube ba, sai bayan wasu shekaru tukun ya fara fitar da ita yana raba sassanta. Dr. Harvey ya raba wadannan sassa na kwakwalwar Einstein sa’annan ya rinka aikawa wasu manyan masana kimiyyar kwakwalwa a duniya suna karantar wadannan sassa daban-daban na kwakwalwa da duba wasu muhimman abubuwa a tattare da ita.

Sakamakon wannan bincike da Dr. Harvey ya gudanar tare da wadannan manyan masana kimiyya ya tabbatar da cewa kwakwalwar masani Albert Einstein daban ta ke da ta sauran mutane a duniya. Dr. Harvey a matsayinsa na wanda yake aikin kwakwalwa tare da manyan masana sun ce ba su taba ganin kwakwalwar da ta ba su mamaki irin ta Albert Einstein ba. Wato wannan bincike ya nuna cewa a cikin wannan kwakwalwa, saboda yanayin girmanta, sashen “parietal lobe” na ta ya karu da kaso 20%, ta yadda karfin tunaninsa da kuzarin lissafinsa suka karu. A bincike na gaba an kara gano cewa jijiyoyin alamun kai sakonninsa sun haura na sauran mutane da kaso 17%, wato wannan na nuna yanayin karfin kwakwalwarsa.

Kwakwalwar Einstein

Dr. Thomas Harvey ya ce gano wadannan abubuwa ne su ka sanya shi sace kwakwalwar Albert Einstein a lokacin da yake kan gawarsa don gudanar bincikensa.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

8 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *