3

Mansa Musa I: Attajirin da ba a taba yin irinsa ba

Mansa Musa

A karni na 13 zuwa na 14 anyi wani attajirin sarki a kasar Mali mai suna Mansa Musa. Kalmar “Mansa” na nufin sarki a lokacinsu.

Wannan attajiri ya rayu na tsawon shekaru 56 zuwa 57 daga shekarar 1280 zuwa 1337. Hakika duniya, musamman Afirka ba za ta taba mancewa da gudunmawar da wannan attajiri ya bayar ba wajen sadaukar da tarin dukiyarsa domin taimakon al’umma.

Wannan attajirin sarki ya kasance mutum mai tausayi da son taimakon jama’a, shiyasa ma ya karar da tarin dukiyar ta sa wajen taimakon mutane. An kiyasce cewa Mansa Musa a lokacin ya mallaki dukiyar da darajarta a yanzu ya kai dalar Amurka biliyan dari hudu da goma sha takwas ($418b) dukiyar da babu wanda ya taba mallakarta a tarihin duniyar zamani tun daga shekarar 1200 har zuwa yanzu, kimanin shekaru 820. Wasu masana tarihi kuwa suka ce a’a, dukiyar Mansa Musa ta wuce adadin yadda za a iya kiyasce ta ma’ana ta wuce tunanin mutum.

Hasashen masana ya nuna cewa bayan Mansa Musa babu wani wanda ya taba rike kusan wannan tarin dukiya sai Jakob Fugger, mutumin kasar Jamus wanda ya rayu daga 1459–1525 a inda ake hasashen cewa ya tara dukiyar da darajarta ayanzu ta kai dalar Amurka biliyan dari hudu ($400b).

Na uku sai John Rockefeller, mutumin kasar Amurka da ya rayu daga 1839–1937 a inda ya mallaki dukiyar da darajarta a yanzu ta kai $350b.

Na hudu sai Andrew Carnegie ba’Amurke da ya rayu daga shekarar 1835 zuwa 1919 wanda yayi sanadiyyar samar da jami’ar Carnegie Mellon University a Amurka da kuma gina kamfaninsa Carnegie Steel Company.

Na biyar sai Osman Ali Khan mutumin Hyderabad na kasar India a inda shi kuma ya mallaki dukiyar da darajarta ta kai $210 a yanzu a inda shi kuma yayi rayuwa daga shekarar 1886 zuwa 1967. Osman Ali Khan a zamaninsa ya zama mutum lamba daya wajen shahara da dukiyar da yafi kowa a duniya.

Wannan kiyasi ne na shekaru daga karni na 12 zuwa na 20

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

3 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *