5

Gudummawar Ibn al-Haytham a Duniyar Kimiyya

masanin kimiyya ibn al-haytham
Ibn al-Haytham

Ibn al-Haytham wanda aka fi sani da Alhazen a yammacin duniya wani shahararren masanin kimiyya ne da aka Haife shi a garin Basra na kasar Iraq, ya kuma rayu a karni na 10 zuwa na 11. Cikakken sunansa Hassan Ibn al-Haytham babban masani ne a bangaren kimiyyar physics bangaren gani (optics), lissafi da kuma kimiyyar sararin samaniya. Ibn al-Haytham shine masani na farko da ya fara yin bayani cewa gani (vision) yana aukuwa ne matukar haske ya daki abu sa’annan ya dawo ga ido, idan aka dauki misalin majigi (projector) wanda haskensa yake dukan jikin allo domin ya nuna wani hoto. Ibn al-Haytham bai tsaya nan ba, shine makasudin wanzuwar kyamara a wannan duniyar tamu.

Wannan babban masani yayi bayani cikakke a cikin shahararren littafinsa “The Book of Optics” wanda yau ya taimaka wajen daukan hoto da bidiyo duk ta hanyar amfani da kyamara. Shine mutum na farko da ya fara kirkirar pinhole camera – wata yar kyamara ce da ta ke zuko abu daga dan nesa domin abun ya bayyanu a majigi bayan la’akari da tsawon abun da nesan da yake tsakani.

fikirar ibn al-haytham

Har ila yau, akwai wata sarkakiya ta lissafi da wannan babban masanin yaso yayi bayaninta ana ce mata Alhazen’s problem, amma tun daga wancen zamaninsa karni na tara ba a samu wanda ya warware ta ba sai Von Neumann a karni na ashirin a shekakar 1997.

Cikin gudummawar da Ibn al-Haytham ya bawa kimiyya akwai:
i. kirkirar pinhole camera
ii. samar da saukakkar hanyar warware lissafin Cauchy-Riemann Integral
iii. samar da Law of cotangents
iv. samar da Ruffini-Horner Algorithm
v. fara gano Wilson’s theorem
vi. bayani kan glass magnification da convex lens
vii. fadada lissafin proof by contradiction
viii. nazari da kawo kimiyyar optic chiasm
…da sauransu

Wadannan sune a takaice gudummawar da wannan babban masani ya bawa duniyar kimiyya da fasaha da fikirarsa. A yau ya kasance duk lokacin da aka tuno da fasahar kymara to ba ta direwa ga kowa sai Ibn al-Haytham saboda cikakkiyar gudummawar da ya bayar.

Ba Ibn al-Haytham kadai ba, akwai manyan masana kimiyyar musulunci da suka yi ruwa-da-tsaki wajen kafa kimiyyar zamani kamar su Ibn Sina, wanda ya bada gudummawa sosai a fannin likitanci; Abbas Ibn Firnas, wanda ya fara kawo fasahar tashi sama wato jirgi; al-Kwarizmi, wanda ya fara kawo lissafin algebra a cikin littafinsa Ilm al-jabr wal-mukabala da kirkiro fikira da lissafin algorithm; Jabir Bn Hayyan, wanda ya zama uba ga kimiyyar chemistry; Al-Zahrawi, shima ya zama uba ga fida (a likitance), Al-kindi, masani a kimiyyar chemistry da ya fara hada turare, Al-Jazari, wanda ya fara kawo fikirar yi-da-kanka wato automatic machine, da sauransu.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

  1. Wannan shine karo na farko dana fara ziyartar wannan shafi kuma tabbas na gamsu kuma ina fatan ci gaba da bibiyar wannan shafi domin naga akwai tarin karuwa aciki AMMA kuma bansan ta yanda zan kasance Na zama memba acikiba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *