4

Me Yasa MTN ya bar Glo a baya?

MTN

MTN da Glo dukkaninsu kamfanonin fasaha ne na layukan wayoyi da suke gudanar da kasuwancinsu a nahiyar Africa musamman ma Nigeria. Dukkanin wadannan kamfanoni sunada kostomomi da dama amma kamfanin MTN yayi wa kamfanin Glo fintinkau a inda yake da kostomomi a kalla 58million a Nigeria kadai, shi kuma glo yake da 45million.

Kamfanin MTN da ke harkokinsa a Nigeria, South Africa, Ghana, Iran,  Cameroon, Ivory Coast, Uganda da sauransu asalinsa ba na Nigeria ba ne na South Africa ne. An kaddamar da kamfanin MTN a Nigeria a shekarar 2001 a inda yake aiki a dukkanin jihohi 37 da ke kasar. An yi ittakafin cewa a yanzu haka ‘yan Nigeria ne mafiya yawa daga cikin masu amfani da layin MTN a dukkanin kasashen da kamfanin ke gudanar da harkokinsa. Kuma kaso daya cikin uku (1/3) na ribar da kamfanin ke samu daga Nigeria ne. Wannan abu yayi matukar ba wa mutane mamaki cewa ta yaya kamfanin da ba ‘yan Nigeria suka yi shi ba amma yafi na asalin kasar bunkasuwa da shahara da kuma samun daukaka fiye da dukkan wani kamfanin layin sadarwa.

Glo

Akwai dalilai masu yawa da yasa wannan kamfani na MTN yafi sauran bunkasuwa da shahara a inda kuma yake samun kostomomi fiye da su. Wasu daga cikin dalilan sun hada da:

  1. Kwarewa wajen tafiyar da kamfani – A zahirance, idan kayi la’akari da ma’aikatan kamfanin MTN na gida da na waje za ka ga dukkaninsu kwararru ne a wajen aiki. Sunada kwarewa sosai wajen samun tasirin shiga kasuwa da bunkasa kasuwanci, sun san dabarun fadada kasuwanci da tafiyar da kamfani yadda ya kamata sabanin yadda sauran kamfanonin suke yi kamar Glo. Kamfanin Glo bai damu da bunkasa kasuwancinsa kamar yadda MTN yake yi ba.
  2. Maida hankali wuri daya – Tunda kamfanin MTN Group babban kamfani ne da ya hada wasu kamfanoni a karkashinsa, wannan ya zama cewa sun ware wasu jajirtattu wajen tafiyar da kamfanin yadda ya dace da kuma tabbatar da bunkasa shi. Shugaban kamfanin Glo, Mike Adenuga, ba ya bada kwarin gwiwwa dari-bisa-dari wajen mayar da hankalinsa domin bunkasa kamfanin da ya kirkira da kansa, a maimakon haka sai ya shiga neman kudi da suna ido rufe. Ba wai a kamfanin Glo kasuwancinsa ya tsaya ba, yana harkallar mai (oil & gas) da sauransu wanda kuma hakan yake kara tabbatar da cewa shi ba kamfanin tsura ne a gabansa ba sai dai neman tara kudi. Idan ka duba yawancin attajiran Nigeria harkar mai suke yi, dan haka shima ya fada harkar saboda kudi amma bai kula harkar fadada kamfaninsa na Glo a inda abokan kasuwancinsa suka masa fintinkau.
  3. Tsarin ma’aikatan kamfani – Duk da tsarin ma’aikatan kamfanin Glo yana tafiya yadda ya kamata, amma na MTN ya fi nasu nesa ba kusa ba. A tsarin gina kamfani da kuma neman ma’aikata, ana neman hadin kan ma’aikatan ne ta yadda za su taru domin cimmawa kamfanin kudurorinsa ba wai wadanda za su samu abunda suke nema kawai su yi tafiyarsu ba.
  4. Bunkasa kasuwanci da janyo masu ciniki – Yadda kamfanin MTN yane shiga lungu da sako yana bunkasa kasuwancinsa, kamfanin Glo ba yayi. MTN suna shiga kauyuwan da ke lungu suna kafa kasuwancinsu kuma suna inganta shi ta yadda ba a yawan samun matsala kamar yadda ake samu da Glo. Suna amfani da wasu dabaru domin kara janyo kostomomi kuma sunada ingantattun kayan aiki shiyasa kamfaninsu yayi nisa.
  5. La’akari da yanayin kasuwa – Ana la’akari sosai da nau’i da kuma yanayin kasuwanci tare da duba sosai ga abokan kasuwanci domin a fahimci hanyoyin da ya kamata a bi wajen bunkasa kasuwanci. Ba lallai bane in kamfanin Glo yana daukar darussa akan wasu abubuwa da yayi da kuma yadda zai fuskanci na gaba. Kamfanonin da su ka ci gaba suna la’akari da wace irin riba da faduwa su ka yi a wata ko shekara sa’annan su duba yanayin yadda za su kara bunkasa kasuwancinsu ta hanyar ribar da kuma yadda za su gujewa hanyar faduwar da su ka yi.
  6. Kayan aiki da tafiya da zamani – A yanzu yadda kamfanoni suke kokarin sanya abubuwan zamani da tafiyar da kamfanoninsu da kayayyakin aiki na zamani, har yanzu an bar Glo a baya. A kullum kamfanonin fasaha na kasashen waje suna ka kafa komiti na masana fasahohin zamani akan binciken da za su yi da yadda wannan kamfanin zai mallaki wannan fasahar da kuma yadda za su bunkasa kamfaninsu ta hanyar wadannan tsare-tsare na zamani. Amma a nan nahiyar Africa musamman NIgeria, har yanzu wadannan matsalolin na rashin zamanantar da abu auna kara ci gaba.

Duk da wadannan dalilai kadan, har yanzu ana kara la’akari da wasu abubuwa kamar jimawa a kasuwanci wanda hakan ya zama wajibi a wasu lokutan. Misali kamfanin Facebook ya samu MySpace yana tashe a lokacinsa amma hakan bai hana Zuckerberg kaddamar da kamfaninsa na Facebook ba saboda sanin cewa kasuwa ta kan iya chanjawa. A hankali kuwa Facebook ya taso ya shafe zamanin MySpace tare da duk wasu kamfanoni da suke bayan shi.

Idan ka yi tunani za ka fahimci cewa ko da Facebook ya dauki wasu matakai na bunkasa kasuwancinsa kuma ya wuce sauran kamfanonin, to irinsu MySpace basuda wasu abubuwa da mutane suke bukata ne (wato ma’aikatan MySpace sun kasance drone entrepreneurs ne ba su damu da bunkasa kasuwancinsu a zamanance ba). Wannan dalili ya sa kamfanoni da dama sun rushe a duniya kuma da dama suna kan rushewa.

A nan, duk da cewa  kamfanin MTN yanada karfin gaske a wannan nahiya kuma har ya ratsa kasashen turai, cigaban Glo a yanzu a Nigeria da ya kai shekaru 17 yayi kadan. Idan kayi duba ga wadannan dalilai kadan a sama za ka fahimci wasu abubuwa a tattare da hakan.

Ko sana’arka ba ta shafi yanar gizo ba, to ka shigo da ita ka nuna cewa ka tashi wajen bunkasa ta. Watakila a unguwarku kawai aka san kana sana’ar cosmetics, idan ka shigo da ita yanar gizo sai mutane da dama su sani kuma ko da ba za su saya ba za su ba wa wasu na kusa da inda kake kasuwanci shawarar sayan kaya a wajenka.

Kamfanoni da dama da haka suka tashi, kaima kada ka tsaya kallon ruwa kwado ya ma ka kafa.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

4 Comments

  1. Gaskiya kuna kokari musamman wajan fahimtar da Al-umma yadda duniya take tafiya da zamani

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *