8

Tarihin ‘Dinosaurs’ da Halakarsu

Mutane da dama suna yawan tambaya game da wadannan halittu wadanda  ake kira da dinosaurs. A takaice dai dinosaurs wasu halittu ne masu girma da ke kama da ‘kadangare wadanda suka yi rayuwa a duniyar earth na sama da shekaru miliyan 250.

Dinosaurs

Wannan yana nuna cewa sun rayu ne a wannan duniyar kafin mutum da sauran halittun da muke rayuwa da su a yanzu. Abunda ya sa duniya tafi nuna damuwa kan sanin rayuwar dinosaurs shine yadda lokaci daya duka suka mutu babu saura wanda ya rayu. Wannan lamari ya faru ne shekaru miliyan 65 da suka gabata sakamakon wani iftila’i da ya auku a wannan duniyar.

Asteroid

Masana sunyi kokarin gano wannan wane lamari ne ya faru da yayi sanadiyyar halakar dinosaurs wanda daga karshe shahararru da dama suka yi ta kawo nazariyyoyi kala-kala da ke nuna sakamakon aukuwar hakan. Nazariyyar da ta fi dacewa da abunda mutum yake tunani shine fadowar wani dutse da ke yawo a sararin samaniya wanda kan iya zama “asteroid”, “comet” ko “meteor”. Wadannan abubuwa dukkansu da zaran an samu akasi sun fada wata duniya to su kan iya rusa kusan duk wani abu mai rai saboda tarwatsin wuta da za su yi sakamakon fashewa. Tun daga karni na baya har zuwa yanzu wannan nazariyya ta masana kimiyya Luis da Alvarez ita ce ke rura wuta a duniyar kimiyya game da iftila’in da yayi sanadiyyar halakar da dinosaurs. Masana tarihi sun fara gano rayuwar dinosaurs ne ta hanyar dadaddun kayan tarihi (fossils) da kuma gwajin wadannan abubuwa.  Masana sun ce dinosaurs sun zauna ne a dukkanin nahiyar da ke duniyar earth.

Fossil din dinosaur
Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

8 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *