2

Nostradamus: Tarihinsa da Ma’anar “Psychic Power” a Ilimin Psychology

Cikakken sunansa Michel de Nostredeme wanda aka haifa a shekarar 1503 a garin Provence na kasar France. Nostradamus ya kasance likita wanda yake da wata irin baiwa ta sanin abunda zai faru nan gaba (hakikancen hangen nesa, ‘prophecy’).

Mutane da dama suna yi masa kallon mahaukaci sakamakon yawan zaman da yake yi shi kadai yana rubuce-rubucen baituka cikin wani littafin da ya sanyawa suna Les Propheties (The Prophecies), wanda ya kunshi baituka 942. Amma mafi yawancin mutanen zamaninsa suna yi masa kallon matsafi ne ko mai kambun baka, saboda idan ya fadi abu to sai ya faru.

Hakika Nostradamus ba matsafi bane ko maye (kamar yadda gargajiya suke cewa). Binciken wannan zamani bai yi zurfin gane halayen Dan-Adam ba (Psychology), dan haka daga baya masana suka jefa Nostradamus cikin jerin psychic (wato mutumin da yake da wani dan tabin hankalin da ya janyo yana iya yin hakikanin hangen nesa ko gano wani boyayyen sirri ko wani abunda mutane ba za su iya sani ba.

A ilimin kimiyya yawancin mutanen da suke cikin irin wannan yanayi ana ce musu psychic sabanin yadda gargajiya suke dangantasu da mu’amala da aljanu).

Nostradamus ya ci gaba da sana’arsa ta sayar da magani kuma a matsayin masanin kimiyyar taurari (astrologer) a inda yayi aure a shekarar 1531 kuma suka haifi ‘ya’ya biyu tare da wannan mata tashi ta farko. A tsakanin shekarar 1534 zuwa 1535 ne yayi tafiya zuwa wani gari domin yi musu magani sakamakon wata cutar annoba da ta balle, amma bayan dawowarsa gida sai ya tarar iyalansa duk sun mutu sanadiyyar wannan annoba a shekarar 1535. Wannan abu ba karamin tada wa Nostradamus hankali yayi ba, har yayi ta fada da sauran likitoci da mutanen gari akan kin ceto rayuwar iyalansa da suka yi har ta kaisu ga mutuwa. Daga nan ya rubuta wani kundi wanda ke dauke da jerin bayanai game da ilimin taurari wanda a zahirance ke nuna wasu abubuwan da zasu faru nan gaba. Sakamakon daukakar da wannan kundi ya samu sai ya ci gaba da rubuce-rubuce kan abubuwan da zasu faru nan gaba (daga zamaninsa har zuwa daruruwan shekaru gaba), kuma daga baya ya tare zuwa bayan gari sannan ya ci gaba da wannan rubuce-rubuce mai kama da baituka kuma ya tattara su waje daya ya samar da littafinsa na Les Propheties, sannan ya wallafa shi a shekarar 1555.

A da mutane sun dauka kawai hauka yake rubutawa tunda sun dauka ya samu tabin hankali ne, sai bayan wallafa wannan littafi suka rinka ganin abubuwanda ya rubuta suna faruwa, sannan sai dubunnan mabiya suka bi baya. Abubuwan da Nostradamus ya rubuta har yanzu suna faruwa. Daga cikin abubuwan da wannan masani yayi hangen nesan faruwarsu akwai:

1. Harin 9/11

9/11 Attack

“9/11 Attack” (harin da aka kai cibiyar kasuwanci ta duniya da ke kasar United States a ranar 11 ga watan September a shekarar 2001) domin ya rubuta a cikin littafinsa cewa:

“Wuta mai girgiza kasa za ta tashi a sabon birni (New City). Manyan duwatsu guda biyu za su hargutse na tsawon lokaci…’

Abunda ya faru shine a wannan rana da safe wannan dogayen binaye guda biyu (manyan duwatsu guda biyu) na cibiyar kasuwanci ta duniya a garin New York (sabon birni) suka rushe sakamakon wannan hari da kungiyar Al-qaida da ta kai.

2. Rayuwar Adolf Hitler

Hitler

Nostradamus bai tsaya nan ba domin sai da ya rubuta a cikin wannan littafin nasa game da rayuwar Adolf Hitler:

“Za a haifi wani yaro daga gidan talauci a can yammacin turai, mai harshen nasara cikin jami’ai, daukakarsa za ta kewaya har gabashin duniya, Adolf Hisler”

Anan an samu kuskuren rubutu ne ya rubuta Hisler sabanin harafin  “t” din da zai samar da Hitler. An haifi Adolf Hitler a shekarar 1889 a Austria wanda take can yammacin turai, kuma sakamakon yakin duniya da yayi na biyu yasa Nostradamus ya kirashi da “mai harshen nasara cikin jami’ai”

3. Mutuwar Sarki Henry na biyu (King Henry II)

King Henry II

Ya ce “Matashin zaki zai kawar da tsohon a fagen daga, raunuka biyu za su samar da daya, sannan sai yayi mutuwa mai kuna”

A shekarar 1559 Sarki Henry II (tsohon zaki) ya ja daga da Comte de Montgometry (sabon zaki), wanda sarkin ya bashi tazarar shekaru 6. A wannan lokaci kuma an taru ne domin shagalin bikin ‘yar wannan sarki. Daga nan ne shi Montgometry ya kutsa kan fuskarsa har yayi nasarar samun idon wannan sarki. Dudda irin namijin kokarin da likitocinsa sukayi, sai da Henry ya kamu da ciwo mai tsanani (sannan sai yayi mutuwa mai kuna), kuma ya mutu a gidansa bayan kwanaki 11 da faruwar wannan al’amari.

Wasu daga cikin hangen nesan Nostradamus wanda suka faru sun hada da; juyin-juya hali na France (1789), gano kananan kwayar halitta ta “bacteria (Na Louis Pasteur), Charles De Gaulle, fashewar bam din Hiroshima da Nagasaki, mutuwar sarauniya Diana da sauransu.

Nostradamus ba shi kadai bane mutumin da yake amintaccen hangen nesa (prophecy) ba, akwai irinsu Jeane Dixon (1904-1997), Daniel Dunglas Home (1833-1886), Edgar Cayce (1877-1945), Ted Serios (1918-2006), Peter Hurkos (1911-1988), Jane Roberts (1929-1984) da sauransu. Masana kimiyya a bangaren sanin halayyar Dan-Adam sun danganta irin wadannan mutane da matsayin wadanda suke da “psychic power”, wanda duk suke a bangaren “paranormal activities” (wani lokaci “psychic activities”). Akwai wadanda suke iya magana da juna ta zuciya (telephatic communication), sanin wani sirri da yake boye (clairvoyance, extrasensory perception), cire wata cuta a jikin mutum ko sanin abunda yake damun mara lafiya daga kallonsa (psychic surgery, remote viewing) da sauransu.

Baiwar hangen nesa ta Nostradamus da “psychic activities” na daya daga cikin hujjojin nazariyyar theory of the cosmic phenomena wacce nake da alhakin gina ta.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *