5

Me Yasa Muke Rayuwa a Duniyar Earth?

Abun tambaya ne babba kasancewar tsintar kanmu da muka yi muna rayuwa a wannan duniya wacce daya ce daga cikin duniyoyi takwas da muke dasu a “solar system” dinmu. Har yanzu masana kimiyya ba su gama gano inda rayuwa ta fara a falaki ba, sai dai ana tunanin ta fara ne a wannan duniyar da muke ciki kimanin shekaru biliyan hudu da miliyan dari (4.1 billion years) da suka shude idan muka yi la’akari da samuwar duniyarmu wajen shekaru biliyan hudu da miliyan dari biyan (4.543 billion years) da suka shude. Duk da haka wasu masana kimiyyar sun tabbatar da samuwar rayuwa ne shekaru biliyan uku da miliyan dari biyar (3.5 billion years) da suka shude bayan la’akari da wasu dadaddun “fossils” din da ake tunanin za su kai akalla shekaru biliyan uku da miliyan dari bakwai (3.7 billion years).

Planet Earth

Shekaru biliyan shida (6 billion years) da shuka shude kuwa babu tunanin samuwar wannan duniya tamu hatta tsarin hasken ranar mu. Bincike ne ya tabbatar da cewa sakamakon haduwar wasu sinadarai ne aka samu dukkanin duniyoyin da suke a “solar system” dinmu.

Karanta: Mu leka Blackhole (1), (2)

Shahararren binciken masanin kimiyya Robert Hooke akan “cell” a shekarar 1665 shi ya tabbatar da inda kwayar halittu su ka samo asali, kafin daga baya a shekarar 1839 wasu masana kimiyya Theodor Schwann da Jakob Schleiden su ka gina nazariyya akansa cewa shi ne jigo na rayuwa kuma duk wata halitta ta samo asali ne daga shi. Mafi yawan bincike ya tafi ne akan farkon abu mai rai a duniyar earth shine “prokaryotic cell” wanda ake tunanin bayyanarsa kusan shekaru biliyan hudu (4 billion years) da suka shude, kimanin shekaru miliyan dari bakwai da hamsin (750 million years) bayan samuwar ita kanta duniyar. Sai dai masana kimiyya sun kara binciko wasu “fossil” din da ake tunanin zai iya kaiwa shekaru biliyan uku da miliyan dari bakwai (3.77 billion years) zuwa biliyan hudu da miliyan dari biyu (4.2 billion years), kenan hakan yana nuna cewa rayuwa ta samo asali ne shekaru kadan bayan samuwar wannan duniyar. Idan har wannan bincike ya tabbata cewa dadadden “fossil” din da aka gano a shekarar 2017 a kasar Canada mai suna “Hematite Tubes’ ya kasance yanada shekaru biliyan uku da miliyan dari bakwai (3.77 billion years) zuwa biliyan hudu da miliyan dari biyu (4.2 billion years), to kenan rayuwa ta fara ne cikin kankanin lokaci bayan samuwar farkon teku a wannan duniyar. Sai dai a farkon shekarar 2018 ne masana kimiyya suna kara binciko wani dadadden “meteorite” mai suna “Northwest Africa 11119” wanda ake tunanin ya kai kimanin shekaru biliyan hudu da miliyan dari biyar (4.5 billion years) dauke da ruwa da kuma wani sinadarin “organic compound”. Daya daga cikin masu binciken wannan “meteorite” ya shaida cewa “wannan ‘meteorite’ din da muke karanta ya sha bam-bam da duk wani ‘meteorite’ da aka sani”, Daniel Dunlap daga cibiyar karantar ‘meteorite’ a jami’ar Arizona State University.

Northwest Africa 11119

Har ila yau, bincike ya kara tabbatar da asalin samuwar ruwa a wannan duniyar shekaru kadan bayan samuwarta sakamakon haduwar wasu sinadarai, dalilin da yasa muka fi sauran duniyoyin samun ruwa kasancewarmu kebabbiyar duniya. Samuwar ruwa a wannan duniya shi zai bamu amsar tambayarmu meyasa muke rayuwa a wannan duniya?, anan zamu daidaita lokacin samuwar rayuwa daga ruwa. Kashi 80 cikin 100 na “cytoplasm” din “animal cell” ruwa ne, kenan rabi da kwata na sinadarin rayuwa ruwa ne. Samuwar ruwa a wannan duniya ne yasa muke samun ruwan sama bayan wani gajeren mataki na “water cycle” da kuma chanjin yanayi wanda sune suka habbaka wanzuwar rayuwa har izuwa wannan lokaci.

Karanta: Tarihin Dinosaurs da Halakarsu

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

5 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *