1

Wace Sana’a Zan Yi a Yanar Gizo?

Lokuta da dama matasa suna yawan tambayar me ya kamata su koya idan an zo bangaren koyon fasahohin zamani da sana’o’i, amma saboda rashin sanin yaya suke da kuma amfaninsu da yadda za su fara sai suke zubar da gwiwwa. Yanzu buri na shine fayyace wasu daga cikin sashinan fasaha da ya kamata matasa su sani domin koya, wanda a takaice kuma a kalla ko ba a fannin fasaha a na’ura kake ba to za su iya taimaka maka domin ginuwa da kanka da dai sauransu.  

Karanta: Mu Fahimci Fasahohin Zamani – Kashi na daya, kashi na biyu, kashi na uku da kashi na hudu.

A matsayinka na matashi ya kamata ka samu kwakkwarar hanyar da za ka rike domin zama mai amfani gare ka ta bangaren ginuwa da kanka ba biyewa wasu shafukan wucin-gadi ba wadanda za suyi maka alkawarin ninka maka kudi idan ka tura musu; wadannan duk harkalla ce ba mai dorewa ba, mai cike da damfara da rashin yarda. Idan da zaka ba wa kanka lokaci ka koyi ko kadan ne daga cikin wadannan abubuwa sa’annan ka rike su a matsayin fannin da za ka rinka samu, to hakika za ka iya dacewa da yardar Allah. A cikin littafi na eBillions Mastery na lissafo wadannan hanyoyi da fasahohi da ya kamata mu bi:

1. Create and Own a Startup

Za ka iya kirkirar kamfani domin zame maka hanyar samu. Kamfani ba sai wata babbar ma’aikata mai cike da ma’adanai ana sarrafawa ko ma’aikata ba, a’a kamfani kan iya zama ginanne ne idan mai shi yanada hikimar da zai iya mayar da shi haka. Kamfani kan ginu ne idan mai shi yanada ‘mission’, ‘goal’, ‘plan’ da ‘strategy’ na abunda zai rika a kamfanin wato gundarinsa. Ka kan iya bude shafin yanar gizo ya zama kamfaninka ta yadda zaka rinka tafiyar da tsarukansa da wadannan abubuwa. Yanzu kamar Naijaloaded, Nairaland da sauransu kamfanoni ne masu zaman kansu duk da ma ginannu ne, to haka kai ma zaka iya farawa kamar yadda suka fara. Anan, idan har kanaso ba wai sai kanada ilimin kirkirar shafuka ba, za ka iya daukar hayar ‘yan kadago domin su gina maka sa’annan su damka shi hannunka kai kuma ka ci gaba da rike abinka. Ka na iya daukar dan kadago ma ya rika lura maka da shi idan kai kana ganin abun zai iya baka wahala kafin kai ma ka samu ilimin da zaka rinka lura da shi.

Karanta: Me ya Kamata ka Sani Dangane da Gina Kamfani?

2. Blogging/Vlogging

Kada ka tsaya cewa kai ba zaka iya ba, kayi sani cewa a yanzu duniya ta ci gaban da ya wuce tunanin mutum. A yanzu haka za ka iya bude hanyar samun kudinka ne idan ka koyi wadannan fannoni na rubutun yanar gizo da kuma daura bidiyo a shafinka ko a tasharka ta YouTube. Wadannan hanyoyi a takaice sun zama ruwan dare kuma a yanzu ba karamin samu ake da su ba. Za ka iya farawa ta hanayar koyon yadda wadannan abubuwa suke wakana da kuma yadda za ka iya tafiyar da naka idan ka bude.

Karanta: Samun Kudi a Yanar Gizo: Me Zaka Iya Sani Daga Cikin Content Marketing

3. Graphics Design

A yau wannan bangare na daya daga cikin hanyoyin da matukar ka koya kuma ka rika to babu shakka za ka iya samu mai yawa daga ciki. Za ka iya yi wa mutane katin aure, bidiyo, gyara hoto, ‘logo/banner’, ‘business card’ da sauransu wanda za ka iya tara kudade da dama akan wannan aiki matukar ka koya yadda ya kamata. Za ka iya farawa da Photoshop da CorelDraw a na’urarka kafin daga bisani idan ka ci gaba ka samu wasu.

4. Freelancing

Wannan shine aikin kadago. Yana yiwuwa a fannoni da dama kamar zama web/software/app developer, writer, business consultant, media analyst da sauransu. Idan ka kware daga cikin wadannan da ma wasu daban to hakika za ka iya samun ba ma na sawa a baka ba, sai dai ma na gina kanka gaba daya. Misali a yau kana iya zama ‘app developer’ ka rinka kirkirarwa mutane manhajoji suna biyanka da dai sauransu. Akwai hanyoyi daban-daban na koyon yadda za ka kirkiri shafin yanar wato ‘web development’ kai ma kuma ka rika kirkirarwa mutane. Wadannan hanyoyi sun hada da koyon yaren na’ura wato ‘programming language’, sanin tsarin tafiyar da shafukan yanar gizo – ‘web mastering‘ da sauransu. Nayi bayani a takaice a kan wannan a wani rubutu na Yaya Ake Zama Developer, idan ka karanta zaka iya samun gamsashshen bayani, ko kuma ka saukar da littafi na Program a Computer to Learn How to Think

5. Online Business

Watakila zamanka a yanar gizo ya baka damar sanin wasu hanyoyi da za ka iya samun kudi sai dai rashin sanin madafa shi yake wahalar da kai. A shawarce, da zaran ka samu wata hanya komin kankantarta to kada kayi wasa da damarka, kawai ka koye ta sa’annan ka fara bayan ka samu wasu abubuwan da ba za a rasa ba kamar sanin matakan fara kasuwanci, jari da kuma nau’in tafiyar da kasuwancinka. Kana iya sayen abu ka sayar a yanar gizo. Kana iya hada hannun jari da ‘yan kasuwa da dai sauran kasuwancin da za ka iya.

Saukar da littafin eBillions Mastery a wayarka domin karanta sauran bayanan da yadda zaka bullo musu.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

One Comment

  1. Gud auwal am very appreciated with your efforts it’s good encouraging of the arewa youth to achieve and develop themself.
    But pls I want upgrade my official
    online business page

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *