9

Menene ‘Social Engineering’ a Duniyar Kutse?

Duniyar kutse tana da hanyoyi da dama wadanda madatsi yake amfani da su domin cimma burinsa wajen yin kutse a wata na’ura, asusun mutane da sauransu. A yau wannan hanya ta ‘social engineering’ ta zama ruwan dare ga madatsa domin kasancewarta hanya mafi sauki da zasu iya samun damar datsar na’urori ta hanyar yaudarar mutane da wani abu. Abun zai iya kasancewa kamar rufa-ido ne wanda mutanen da suka fada tarkon madatsi suke gani.

Menene ‘social engineering’?

Wannan wata hanya ce da madatsa suke amfani da ita wajen yaudarar mutane a bayyane; wato yadda mutum zai yarda da wani abu akasin yadda yake a zahiri wanda yardar ta shi ga abun ne zai jefa shi tarkon madatsa. Wato da sannu mutum zai yarda da abunda wani yake fada masa na yaudara kamar samun damar datse asusunsa na banki ta hanyar yaudararsa cewa za a gyara masa idan ya fada musu (madatsan) wasu lambobinsa na sirri wanda shi bai san da cewa wadannan madatsa ba ne da dai sauran duk wasu hanyoyi na damfarar mutum zuwa ga yarda da abunda zasu fada masa. Wannan hanya ana iya ce mata “mind hacking”

Wasu hanyoyin da madatsa kan bi wajen yaudarar mutane ta wannan hanya sun hada da:

  1. Phishing – wannan hanyar kamar yadda ta zma ruwan dare ana iya amfani da ita wajen yaudarar mutum ya yarda da wani kamar yadda bayani ya nuna a sama wanda ita ma hanya ce mai zaman kanta da ta hada da turawa mutum sakon emel ko likau wanda yake kunshe da ‘virus’ ko wasu manhajoji masu cutarwa ga na’ura. Ta wannan hanya akan iya yi wa mutum datse a asusunsa na banki, fesbuk da sauransu ta yadda zai yarda da wani likau na bogi ya iya sanya bayanansa na sirri a yayinda shi kuma madatsin zai iya daukar wadannan bayanai cikin sauki tunda daman likau din shafin da aka tura masa na bogi ne ba asalin kamfanin ba. Kuma a kan iya turawa mutum wani sako cewa ya samu nasarar cin wani abu kamar kudi ko gasa ko kuma an zabe shi domin samun wadannan daga karshe sai a bukaci wasu bayanansa na sirri wanda za a iya amfani da su wajen shirya masa wani ta’adi. Wannan hanya a kan iya kiranta da “pretexting”
  2. Illusory phishing – duk da wannan ya hada da dukkanin na saman, amma shi har yanzu yana daukar wani bangare ne na jan ra’ayin mutum domin samun damar yin kutse a cikin na’urarsa wadanda suka hada da tura masa malware; domin zama manhaja mai cutar da na’urar, spyware; domin leken asiri da daukar muhimman bayanai a cikin na’ura, ko wani virus; domin zama wata manhaja mai cutar da na’ura wanda ya danganta ga kudirin madatsin. Misali mai sauki ta wannan hanya shine turawa mutum wadannan manhajoji masu cutarwa ga na’urarsa, kuma da zaran ya yarda da wanda ya tura masa har ya sanya su cikin na’urarsa to babu shakka ya fada tarkon madatsi.
  3. Quid pro quo – wannan kuma shine yaudarar mutum cewa za’a bashi wani abu idan shi ma ya bayar; kamar yadda ya faru ranar 15 ga watan Yuli na wannan shekarar a shafin twitter a inda wani madatsi yayi kutse cikin asusun manyan mutane sa’annan ya rubuta cewa duk wanda ya tura masa kudade ta lambar asusunsa to zai ninka masa kudin ya dawo da su. Bayan wannan akwai wasu shafuka da suke ikirarin haka cewa idan mutum yayi rajista da su to za su turo masa ninkin abunda ya tura musu cikin wasu kwanaki wanda daga karshe lamarin yake karewa a damfara.

Wadannan hanyoyi a kalla sun kasance masu matukar hatsari matukar mutum bai kula da su ba, domin fa bahaushe yace “tsuntsu mai wayo ta wuya ake kama shi”, kuma duk mutumin da ya fika wayo to ya kan iya samun damar mallakar tunaninka ta yadda zai iya sarrafa ka yadda yake so.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

9 Comments

  1. Allah yakarawa rayuwa albarka
    Amma malam nakasance dalibi kuma mai matukar son ilimin akan computer Dan allah Idan ga number na ta WhatsApp 09044085376 Idan akwai group asakani pls

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *