0

Mu Fahimci Fasahohin Zamani (4)

Cigaba…

4. VR/AR

Wadannan fasahohi Virtual Reality (VR) da Augmented Reality (AR) masu kamanceceniya da juna a yanzu haka sun shahara matuka a duniya a fannoni daban-daban. Ga su kamar haka:

Virtual Reality

Wannan fasaha ta Virtual Reality (VR) fasaha ce da take kan shahara a duniya a halin yanzu duk da ma ta jima da wanzuwa a kasashen turai can mafararta. Fasahar Virtual Reality a takaice fasaha ce da take nuna wani wuri, yanki ko alkarya wadanda basu kasance a zahirance ba. Hakan yana faruwa ne yayinda mutum ya sanya na’urar a fuskarsa (headset) a matsayin tabarau ta yadda zai rika kallo da ji kamar yana wata duniyar ta daban kamar Dubai ko Paris wanda a zahirance kuma yana dakinsa ne. Ganin abunda wannan fasaha takeyi yasa aka zamanatar da ita ainun domin zama mai amfani a bangarori da daman a rayuwar yau da kullum; kamar karatu, sada zumunci, kasuwanci, wasanni, nishadantarwa da dai sauransu. Misali zaka iya sanya tabarau din fasahar ka iya ganinka a bakin Ka’aba kaima kamar kana dawafi.

Augmented Reality

Fasaha mai kamanceceniya da yar uwarta itace Augmented Reality. Wato ita wannan ta dan sha ban-ban da fasahar VR a inda ita wannan ta ta’allaka ne ga nuna karin wani abu ga inda mutum yake. A nan mutum ba zai ga kanshi a wata duniyar ba face inda yake sai dai zai ga karin wasu abubuwa; misali kamar bayyanar wani abu a gabanshi. Kalmar “augment” na nufin fadada abu, anan “augmented reality” na nufin fadada/karin wasu abubuwa a zahirance ba tare da mutum ya bar ko ya ji cewa yana wani wuri ba. Akwai misalan wannan fasaha a “video games” (wadanda suka shahara a fannin sun san yadda abun yake gudana), sannan “game” din da ya shahara a fannin shine Pokemon Go wanda aka kaddamar a shekarar 2017. Kamfanin ya mayar da kudinsa har ya ci riba sosai bayan sati biyu kawai da kaddamar da manhajar. Sannan sai Google SkyMap da sauransu.

Kamfanonin da suka shahara wajen kirkirar wadannan fasahohi sun hada Microsoft (Hololens), Oculus, HTC, Sony da sauransu.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *