7

Samun Kudi a Yanar Gizo: Me Zaka Iya Sani Daga Cikin Content Marketing

A duniya mun kasance hanyar samun kudi guda daya kacal muke da; itace sayar da abu. Duk wata hanya da zaka samu KUDI a duniya to fa wani abu ka sayar, idan kuwa ba haka ba to babu yadda zakayi ka iya samu. Misali ka kan iya ji ko ganin wasu marubuta na rubuto hanyoyin samun kudi sama da guda 70, 90 ko fiye da haka, kuma a lokacin da kagama karantawa zaka fahimci yawancin hanyoyin makusantan juna ne. Shiyasa na ware wasu ingantattun hanyoyi guda goma sha biyu (12) kacal na samun kudi a cikin littafi na “eBillions Mastery”.

Me yasa nace hanyar samun kudi daya ce a duniya, wato sayar da abu?

A lokuta mabanbanta mutane suna yawan yimin tambayoyi kan hanyoyin da zasu bi su samu kudi a yanar gizo, kasancewar ina bawa bangaren muhimmanci kuma cikin tambayoyin har da content marketing saboda yawan yadda nake karfafa gwarin gwiwa akai. A takaice, zaka iya daukar “content marketing a matsayin safarar kayayyakin yanar gizo – ‘online stuffs’, kamar su rubutu, hotuna, shafuka da bidiyoyi.” Safarar wadannan abubuwa zai baka damar sanin ingancin kowane daga cikinsu, daga cikin wadanda sukafi bawa content marketing muhimmanci sune marubuta. Sanin muhimmmacin rubutu abu ne wanda kowa ya riga ya sani amma iya sarrafa shi ta hanyoyin da ya dace da daukar hankula shine abun la’akari.

A duniyar da muka kasance muna sayar da abu domin samun kudi, kuma mun kasance muna sayar da lokacinmu, iliminmu, da kuma karfinmu. Wadannan abubuwa guda uku (3) sune manyan hanyoyin samun kudi a duniya, kuma dukkaninsu sayarwa muke domin mu iya samun kudi da su. Misali yanzu idan na dauke ka aikin kamfani, ko ‘kadago (freelance) to fa anan ana bukatar ka sayar da iliminka ko karfinka domin samun kudi. Tunda hakane, ashe kuwa samun kudi a wannan duniyar baya wuce sayar da abun.

Tayaya zaka iya samun kudi a content marketing?

Wasu sun dauka daga cewa content marketing kawai wata sana’a ce a yanar gizo wacce zaka je ka rinka samun kudi da ita. Idan har kana daga cikin wadanda suka dauka haka, to a zahirin gaskiya ba haka abun yake ba. Kawai dai muna cewa kasancewarka marubuci content marketing zai baka damar janyo hankulan jama’a izuwa ga kasuwarka, daga nan kuma ka iya samun damar da zaka gina hanyar samun kudinka akai.
Zaka iya samun kudi ta hanyar content marketing a hanyoyi kamar haka:

 • Rubutu
 • Hotuna ko video
 • koyarwa
 • Shafukan yanar gizo
 • Littatafai

…da sauransu a inda zan dan yi bayani kadan akan yadda zaka rinka samun kudi a yanar gizo duk wata ta wannan hanyoyi da content marketing.

Yadda zaka rinka samun kudi duk wata a yanar gizo

Watakila ka kan iya cin karo da irin wadannan tambayoyin a yanar gizo “Yaya zan samu kudi a yanar gizo?” ko kuma kaji ana cewa “Wace hanya zan bi domin samun kudi a intanet”. Mafi yawan irin wadannan tambayoyin suna fitowa ne daga bakin wadanda basu jima suna harkar intanet ba, amma wani lokacin takan iya faruwa wadanda suka jima din ma suna fuskantar irin wadannan matsalaoli na aikin sai-baba-ta-gani. Tabbas ana samun makudan kudade a yanar gizo-gizo, amma duk wanda ya sa rai a samun kudi daga wannan harkar zan bashi shawarwari guda biyu zuwa uku, kamar haka:

 1. Ka kasance mai hakuri da juriya
  Wasu mutane da dama sun gudu sun bar harkar daga farawa sakamakon rashin hakuri irin nasu saboda wasu suna tsorata ne da cewa harkar akwai wahala. Bari in fada maka magana ta gaskiya; tabbas harkar akwai wahala, amma fa kayi sani cewa: “duk abunda aka bashi lokaci kuma akayi hakuri to ana dab da samun nasara akai.” Dan haka akwai mutane da dama wadanda kallonsu da kake a babban matsayi ba wani babban abu bane face hakuri da sukayi da kuma jarircewa dan tabbatar da ganin sun samu nasara. Saboda haka matukar kana neman kudi ko karatu, kai ko ma menene, to dole fa sai an hada da wannan HAKURIN.
 2. Ya zama cewa kanada jari
  Idan zaka fara sana’a to ya zamto cewa kanada jari ko kadan ne a hannu. Rashin jari na daya daga cikin abubuwanda suka hana yawancin matasa cigaba da kasuwanci musamman a yanar gizo. Wasu daruruwan kuma sukan iya bude shaguna a cikin gari amma bayan wani lokaci sai kaga sun rufe shi saboda rashin ishaashen jarin da za’a tafiyar dashi. Kada ka dauka cewa jarin da ake bukata na da matukar yawa har kasa a ranka cewa bazaka iya ba, Malam bahaushe yace: “dan guntun gatarinka yafi sari ka bani”. Misali yanzu idan nace ka bude shagon sayar da takalma, to kaga akwai bukatar samun shagon shi kansa, kudin da za’a sayo takalman a karon farko, da kuma kudin dawainiyar kawo kayan ko kuma kwaskwarimar shago da dai sauransu. To kaga anan lallai muna bukatar jari, amma fa ba wani mai yawa ba.
 3. Ka zama mai jarircewa da aiki tukuru
  Bayan ka tabbatar da cewa kuma kasa a ranka cewa neman kudi zakayi saboda haka sai ka hada da hakuri da jari, to fa duk da haka wadannan abubuwa baza suyi maka wani tasiri ba matukar babu jarircewa da aiki tukuru. Wasu da dama daga cikinmu sun jima suna yin manyan ayyukan da dole sai an hada da hakuri sa’annan a ci nasara, wasu kuwa sukan jingine abun ne ga jari tsantsa. A matsayinka na matashi da kuma mai kokarin ganin y samu cigaba a harkokin kasuwancinsa, to zaifi kyau ace kana yin aiki tukuru domin samun nasara. Babu yadda za’ayi wani abu yazo ya same ka a gida shi kadai ba tare da kaje ka neme shi ba, dan haka in da hali jajircewa akan abu na daya daga cikin dalilan da yasa mutane suke samun nasara a rayuwa.

Bayan ka kammala wadannan abubuwa, abu na gaba da zaka iya sani shine lokaci. Lokaci ma yanada fa’ida matuka, domin kuwa dole sai dashi ake samun daman yin kowane abu a wannan duniyar. Dan haka idan ka shirya zaka iya samun kudi a duka/daya daga cikin wadannan hanyoyi da na lissafo a sama to dole sai ka tanadi wadannan shawarwari da zan zayyano kamar haka:

1.Rubutu

Rubutu abu ne mafi girman gaske wanda mutane kalilan ne a wannan duniya ke da baiwar yinsa cikin hikima da basira, cikin miliyoyin marubutan da muke dasu a wannan duniya. Idan Allah ya hore maka baiwar rubutu zaka iya amfani da ita wajen maida ta hanyar samun kudinka cikin sauki. Misali


I. Zaka iya samun kudi a rubuce-rubucen yanar gizo – blogging: Nasan abu mai yiwuwa ne ka iya jin labarin samun kudin da akeyi a yanar gizo ta hanyar wannan salo na rubutu (blogging), amma kasan da cewa kaima zaka iya samu ta wannan hanyar? Abunda zakayi da farko shine ka bude shafin yanar gizon (blog) sa’annan ka rika zarar zantuka kana shimfidawa tare da gayyato mutane suna karantawa.

II. Zaka iya samun kudi a dandalin WhatsApp ta hanyar rubuce-rubucen labarai: Irin wannan sana’a tafi jimiri ne a wajen jajirtattun marubutan labarun nishadi, kasuwanci, koyo da kuma almara. A yau manhajar WhatsApp ta kasance daya daga cikin manyan dandulan da ake ji da su a duniya ta wajen musayar sakonni cikin sauki, dan haka amfani da wannan tsari zai baka damar samun kudi cikin sauki. Misali ace kana rubuta kirkirarrun labarai (novels) sa’annan kana rabasu ga abokanka da ma wadanda baka sani ba a kyauta. Ka kirkiri dandamali (group) na WhatsApp da Facebook da duk inda kasan sakon zai isa ga mutane sa’annan ka rinka raba musu kana gayyato su domin karanta labarun da ka rubuta. Bayan wani lokaci sai ka sanar dasu cewa kana kan rubuta wani littafinka mai matukar kayatarwa wanda zaka sayar dashi akan kudi kalilan, misali ace N200. Bayan ka kammala rubutawa sai ka aikawa abokanka domin su tayaka da talla. Misali ace a Facebook group naka akwai mutane 5,000, shafinka (page) akwai 10,000 likes, sannan Instagram da kuma YouTube, sai kuma WhatsApp group dinka shima akwai akalla mutane 150, sai wadanda kayi joining.

Yanzu duba:

i. Idan kayi rubutu a shafinka na Facebook akalla 1,000 cikin 10,000 zasu gani, sannan a ciki akwai yiwuwar mutane 30 zasuyi kokarin sayen littafinka. Yanzu mu dauka cewa mutane 20 ne suka saya akan kudi N200, kaga N4,000 kenan
ii. A dandamalinka na Facebook (group) inda kake raba musu littatafai kyauta kuma suke son karanta labarinka, ace kanada membobi 5,000, idan kayi tallan littafin a kalla mutane 20 zasuyi kokarin saya. Yanzu mu dauka mutane 15 ne sukayi nasarar sayen littafin akan kudi N150 tunda membobinka ne, kaga N2,250
kenan
iii. Idan kaje group dinka na WhatsApp ace kanada membobi 150 wanda akwai yiwuwar mutane 35 daga cikinsu zasuyi kokarin sayen littafin, idan ka sayar musu akan kudi N150 tunda membobinka ne zaka tashi da a kalla N5,000

Banda tallanka a shafin Instagram, da sauran shafukan yanar gizo, idan muka hada akwai yiwuwar ka iya samun N10,000 a duk wata akan littafi daya. To kenan rike wannan sana’a da karfin gaske ba karamin riba bace matukar zamu dage.

2.Koyarwa

A yau akwai dubunnan mutanen da suke matukar son su koyi abubuwa da dama a yanar gizo, daukar nauyin koya musu ba karamar riba bace a wajenku baki daya. Shin ka taba tunanin ko kanada damar da zaka iya daukar nauyin mutane wajen koya musu wani abu? To bari in tambayeka shin kanada damar da zaka iya koyama dalibai yadda zasu iya samun maki 250+ a jarrabawar JAMB? A yau mafi yawancin daliban makarantun sakandare suna rubuta jarrabawar JAMB ta shiga makarantun gaba da sakandaren, amma fa kadan ne daga cikinsu ke nasarar haye wannan jarrabawa. Yawancin hakan na iya faruwa ne saboda karancin samun madafa ta karatu, idan ka dauki nauyin dawainiyar koya musu lagon wannan jarrabawa hakika zaka samu alheri akai. Misali da farko ace zaka iya daukar nauyin koyar da wadannan kwasa-kwasan kimiyya Physics, Chemistry, Mathematics, Biology, ko kuma English, Government, Economics, Civic Education, Literature in English, Hausa… Sannan ace ka bude dandamalin WhatsApp ne kana gayyato mutane suna shiga, amma da sharadin biyan kudi kafin shiga (Premium/Membership group), ace kudin shigan N200 ne. Cikin wata guda zaka iya samun akalla membobi 20, kaga idan suka biya N200 zaka samu N4,000 kenan. A cikin wata 3 zaka iya samun membobi 60 wadanda zasu biya N200, kaga ka tashi da N12,000 a wata uku. Idan ka cigaba da kiyascewa lissafin ya kan iya haurawa.

Hanya ta biyu shine koyawa mutane abunda yake shige musu duhu. Misali dangane da abubuwanda suka shafi yanar gizo (samun kudi, SEO, boosting blogging career dss), ko kuwa bangaren da ya shafi abubuwa na na’ura (tsaro, tsare-tsare, kutse dss).

Dukkanin wata hanya da zaka iya samun kudi ya kan jinginewa ne da abubuwa guda uku ko hudu da na lissafo a sama a farkon rubutun. Dan haka na kawo wadannan takaitattun bayanan ne wadanda basu bukaci wani jari mai girma ba, sai dai kadan daga ciki na bukatar kudi kalilan wanda bai wuce na kati ko data ba dan mu’amala da kostomominka.

Fatan samun nasara, Allah ya taimaka, ameen.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

7 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *