4

Yaya Ake Zama Developer?

Duk wanda ya fara tunanin zama developer to ko kadan ne ya fahimci waye developer din da kuma aikinsa, wanda kuma bai sani ba zamu iya cewa developer shine mutumin da yake kirkirar manhaja, shafin yanar gizo ko wata na’ura mai kwakwalwa. Dan haka zama ‘developer’ ya danganta ne da bangaren da mutum ya dauka na ‘computer programming’, ta nan ne mutum zai iya gane wane irin developer yakeson zama. A cikin wani karamin littafi na “Program a Computer to Learn ‘How to Think’” na lissafo wasu shawarwari ga duk wanda yakeson fara koyan computer programming wanda zata kai shi ga zama developer na bangarori da dama. Duk da haka, ga bangarorin da mutum zai iya zama developer a bangaren na’ura kamar haka:
💠 Web Developer – wannan bangaren sune developers masu kirkirar shafukan yanar gizo wato web development. Haka akwai matakan da ake bi kafin zama web developer wadanda suka hada da:

 • sanin programming languages kamar PHP, JS, HTML, CSS, Perl, Python
 • sanin ‘database’ da ilimin yadda ake tafiyar da ita tare da koyan languages dinta kamar su SQL, PDO
 • ilimin networking da sanin yadda yake aiki da shige-da-fice a yanar gizo
 • sanin yadda zaka kare shafin yanar gizo daga masu kutse
 • ilimin yadda zaka iya warware duk wata matsala da kan iya tasowa a shafin yanar gizo

Wadannan sune matakan da ya kamata duk wanda yakeson zama web developer ya bi.

💠 Software Developer – wannan kuma sune masu kirkirar manhaja ta na’ura mai kwakwalwa (software development) ko kuwa wani lokacin wayoyinmu na hannu (mobile development) wato a takaice masu kirkirar application software. Matakan da ya kamata mai son wannan bangaren ya dauka kuma sune kamar haka:

 • sanin programming languages kamar C-family (C,C++,C#…), Java, Python, Ruby, Kotlin
 • sanin database da ilimin tafiyar da ita da languages nata kamarsu SQL
 • sanin yadda na’ura mai kwakwalwa take aiki da mahajojinta bugu da kari kuma da mabanbantan operating system
 • samun ilimin Graphical User Interface (GUI) na programming languages din da mutum ya koya ingantattu
 • sanin yadda zaka iya ‘fixing na bugs’ a manhajarka da sauran matsalolin da kan iya faruwa

💠 System Developer – wannan kuma sune manyan. Wato da zaran mutum ya bar software development to ya kan iya fadawa system development ne dudda ma sunada dangantaka mai karfi, kuma mutum zai iya zama dukkaninsu a lokaci daya, sai dai ana farawa ne da software development. Wato system development shine gina ‘devices’ na zahiri (developing real life systems) ta hanyar amfani da wasu microcontrollers, misali shine kirkirar ‘robot’. Mutum yana farawa ne da ‘embedded systems’ kafin yayi nisa har ya kai matakin da zai iya gina shi sakagon, wadanda duka suka ta’allaka ne da gina system din sai dai mataki-mataki ne. Nan ma abubuwanda mutum ya kamata ya sani sune:

 • fadada bincike akan programming languages kamar C, C++, Python
 • gogewa a gina embedded systems (fara aiki da su Arduino ko Raspberry Pi zai fi)
 • sanin ilimin operating systems da yadda aka gina su, da kuma yadda zaka iya manipulating dinsu ka iya amfani da su a naka system din
 • samun ingantaccen ilimin electronics a aikace da kuma a fadance (practically and theoretically)
 • samun ilimin warware matsalolin da kan iya tasowa, kamar su bugs, attack…

Wadannan sune matakan da mutum zai bi kafin ya zama ‘developer’! Sai dai kamar yadda mai karatu yake gani a sama na lissafo bangarori da kuma matakansu, anan zaka iya zaba ka fara ko yanzu ne.

Allah ya taimaka!

Mohiddeen Ahmad
10th May, 2020.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.

4 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *