6

Wasu Shawarwari akan Tsaron Na’ura

Manyan masana sun shaida cewa duk inda kaga an kutsa cikin wata na’ura to laifin mutane shine ke daukar kaso mafi tsoka, a kalla 95%. Na’ura babu ruwanta zata kula maka da kayanka, amma da zaran an samu wata matsala to ka fara bincikar kuskuren mutane; watakila bangaren ma’aikatanka, ko kai kanka ko waau daban, amma ba na’ura a karon farko ba.

Ina matukar mamaki yadda mutane suke ajiye sensitive information da kudade masu a yawa accounts dinsu kuma suna amfani da lambobin tsaro masu sauki. Misali ka kai wayarka chaji kuma lambobin tsaronka sunanka ne, ko date of birth naka ko sunan yarinyarka da sauransu… sai wani yayi nasarar daukar wayarka ya bude, ya shiga account naka zaiyi transfer kudi zuwa nashi a nan ma ya tarar kana amfani da weak password kamar na baya, sai ya sace maka kudi… tsakani da Allah tayaya zaka fara kama shi da irin wannan tunanin naka na sanya lambobin tsaro masu sauki? Laifin waye a karon farko?

A zahirin gaskiya wannan abun ya jima yana faruwa kuma har yanzu. Sa’annan da yadda yan damfara suke samun galaba akan mutane suna kiransu a waya wai su fada musu lambobin sirrunsu na asusun banki da sauransu. Yanzu a matsayinka na wanda ka fahimci hakan, ya kamata ka dauki nauyin fahimtar da wasu mu gudu tare mu tsira tare.

Akwai shawarwarin da masana suka bayar na cewa da zaran munyi amfani da su to yawaitar yi mana kutse zai iya raguwa ko kadan saboda yawancin matsalolin daga gare mu ake samu.

Ana yi wa mutane kutse ta hanyoyi da dama, ya dai danganta ga abunda akeson yi wa kutsen ne. Ga wasu shwarwari da ya kamata mu bi don kare kawunanmu daga fadawa tarkonsu:

  1. Ka koyi rike sirri
    Ka ajiye sirrukanka wadanda za’a iya yi maka kutse da su (sensitive information) a sirrance. Sensitive information sune kamar credit card numbers, passwords, date of birth, security questions/answers, OTPs da sauransu. Wani lokacin sai kaga mutum ya sayar da na’urarsa kuma akwai wadannan sensitive information din a ciki, ko kuwa yana bawa wasu su kai tsaye, ko barinsu wasu suna gani a fili. A zahirin gaskiya wannan kuskure ne.
  1. Kada ka ajiye sirrukanka kara zube – Abun nufi anan shine kada ka ajiye sensitive information a na’urarka kara zube ba tare da ka sanya wasu dabarun boyewa ba kamar encryption, sanya password wajen bude su da sauransu. A shawarce ka nemi takarda ka rubuta copy na su zai fi akan ajiye su a cikin na’urarka.
  2. Kada ka kasance mai yin amfani da lambobin sirri masu sauki – Wannan kuma shine ruwan dare. Misali: 12345, 0000, ranar haihuwa, sunanka, sunan yarinyarka dss wadannan sune misalan lambobin sirri masu saukin canka wanda mafi yawan wadanda suke amfani da su mata ne. Ka kasance mai sanya lambobin sirri masu tsauri hade da symbols, capital/small letters, numbers dss.
  3. Kada ka kasance mai saurin sanya duk wata manhaja a cikin na’urarka – Akwai manhajoji masu hatsari wadanda suke yawo a yanar gizo, wanda kuma yawanci mutane suke fadawa tarkonsu ta hanyar sauke su a cikin na’urorinsu. Kayi hankali da wannan, hakan yana jawowa manyan kamfanoni ma barazana mai tsauri, kuma yayi sanadiyyar sanya mutane da dama cikin hatsari.
  4. Ka rinka kulle wi-fi, bluetooth, location din na’urarka idan baka amfani da su – Akan iya shiga na’urarka ta wadannan hanyoyi ko da baka sani ba. Ka rinka kulle su (turn off) idan baka amfani da su domin gujewa fadawa tarko.
  5. Kayi hankali yayinda ka shiga yanar gizo – Ba kowane link zaka rinka latsawa yayinda kake browsing a yanar gizo ba. Wani lokaci akan iya tura maka link ta facebook, email, whatsapp ko kuma ka gani a wani website ana cewa ka danna ka shiga, idan kuma lamarin yazo da tsautsayi sai a samu matsala. Kayi hankali sosai da irin wadannan domin suna da matukar hatsari, yanar gizo duniya ce wacce ta tara mugaye da muminai wadanda bazaka iya banbance su ba.

Idan har muka bi wadannan shawarwarin da wasu ma, Insha Allahu zamu iya rage saukin yi mana kutse da akeyi da kuma damfara wanda ta zama ruwan dare a yanzu.

Allah ya kare mu, ameen.

Mohiddeen Ahmad
8th June, 2020

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and a writer. I am the founder and CEO of Flowdiary.