2

Mu leka Blackhole (2)

A shekarar da ta gabata ne masana sukayi nasarar daukan hoton black hole na farko a duniya.

Wannan nasara ta girgiza wasu a inda ta sanya musu shakkun tayaya ma aka fara saninsa shekaru da dama baya bale har a yau duniya ta dauki hotonsa na farko? Wato kimiyya tana tafiya ne da kageggen labari (sci-fi) da kuma tunani (imagination) ta yadda marubuta zasu tsara wata tatsuniya kamar ta gizo da koki kana daga bisani sai ayi la’akari da ita a kimiyyance, sai a iya hasashen cewa hakan fa zai iya faruwa, sai a dauki aniyar bincike akai kuma mafiya yawan lokaci ana samu ana tabbatarwa. Haka akayi a lamarin “aliens”, “parallel universe” – wato yanzu ace muna rayuwa a wannan kaunun (universe) wacce ta kunshi solar system dinmu a inda kuma duniyarmu kadai ce inda halittu zasu iya rayuwa kuma sukeyi, shin bama tunanin cewa mai yiwuwa akwai wata duniya bayan wannan inda wasu halittu suke rayuwarsu daban ba? Dan haka akace to mai yiwuwa wannan labarin ya iya zama gaskiya dan haka aka kimiyantar dashi shiyasa ake cewa mai yiwuwa aliens din suna rayuwa ne a wata kaunun (parallel universe). Ka bincika UFO mystery.

Haka zalika shi kansa blackhole asalin samuwarsa tazo ne a irin wannan tunanin (imagination) da ma sauran abubuwan kimiyya. Shiyasa masanin da ya fara tunanin samuwar blackhole a shekarar 1916 a cikin nazariyyarsa ta relativity wato Prof. Albert Einstein yace tunani shine makasudin samuwar ilimi a duniya. Sannan cikin manyan masanan da suka maida hankali wajen binciken asalin blackhole, nau’insa da kuma yanayinsa sun hada da Prof. Hawking, amma naso ace lokacin da akayi nasarar dauko hoton blackhole bai mutu, sai muji wane irin sharhi zaiyi akai.

Einstein a cikin nazariyyar tasa ta relativity yace maganadiso (gravity) yana ta’allaka ne da lokaci (time) da kuma wuri (space). Anan ya nuna cewa lokaci a kaunu baya tafiya ne a kai daya, misali mai sauki shine a yayinda mukayi tafiya izuwa sararin samaniya to yanayin lokacinmu da wadanda suke rayuwa a duniyar da muka bari (earth) daban ne.

Masanin kimiyya Prof. Edward Teller ya kara jaddada bayanin Einstein cewa da ace zamuyi tafiya zuwa wajen tauraro to muna bukatar abunda (spaceship) zaiyi gudu kamar haske (speed of light), ta yadda zamu iya kaiwa ko da Milky Way dinmu ne a cikin miliyoyin shekaru (sai dai zai banbanta ainun akan yadda ake tunani). Yace sai dai a lokacin da muka dawo duniyar nan ko da ace shekaru 5 mukayi (a can) to anan za’aga kamar munyi shekaru 50 ne. Kenan a saukake a can lokaci baya tafiya kamar yadda yake gudu anan, kuma haka lamarin yasha banban ko da a duniyoyin mu ne (planets) da yanayin zagayensu (rotation and revolution around the sun).

Da yake nazariyyar tasa tanada fadi sosai (special relativity da general relativity) wanda har ya mata formula mai zaman kanta wacce ta shahara a duniya ainun wato mass-energy equivalence (e = mc²). Anan ya fadi abubuwa da dama kuma ya karfafawa masana kimiyya gwiwwa cewa zamu iya zuwa har can gungun taurari. Nace kan ku kawai akeji ai ni tuni naje Milky Way na dawo 😊

Edward Teller yana cewa bai fidda rai ko da ace bayan shekaru 500 ne ba matukar aka samu abunda zai iya gudu kamar haske to mutum zai iya zuwa gungun taurari ko da ace namu ne (Milky Way). Yace sai dai matsalar bamu sani ba ko guzurinmu na nan ya iya zama guba (poison) a can saboda canjin lokaci, wuri ko wasu boyayyaun sinadarai.

A yau babu wani abunda ya kai haske gudu domin yana tafiyar kilometer 300,000 a cikin dakika daya (300,000km/s), sai dai sabon bincike ya nuna cewa idan spaceship zai gudu kamar haske (travelling at the speed of light) zai iya zuwa Milky Way galaxy a shekaru 200,000 a hakan din ma itace mafi kusa damu, itace tamu ita muke iya gani. Gungun taurari mafi nesa damu kuma shine MACS0647-JD, wanda idan za’a aika haske sai ya kai shekaru 13.3billion kafin ya karasa, ba fa shekarun mu na nan ba, shekarun haske (light year) wanda haske yana tafiyar kilometer 9.461 trillion a shekara daya, to sai ya shafe shekaru 13.3bn kafin ya kai MACS0647-JD galaxy.

Tsarki ya tabbata ga mahaliccin da yayi kaunu da abunda ke cikinta!

✍ Mohiddeen Ahmad
21st May, 2020.

Mohiddeen Ahmad

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad, an inquisitive student, tech aficionado, science enthusiast and writer. I am the founder of Flowdiary.

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *