0

Madogaran Nasara (5)

Cigaba…

8. Mark Zuckerberg
Mark Zuckerberg ya kirkiri shafin Facebook a shekarar 2004 lokacin da yake karatu a jami’ar Harvard da ke America. Lokacin da yaga ya samu wata dama na daukaka shafin sai wani mutum anace masa Peter Thiel ya zuba masa hannun jari a kamfanin anan ya samu kudin da ya gina shago ya kuma mayar dashi ofishinsa a Palo Alto. Ganin wannan damar yasa ya watsar da harkar karatunsa na jami’a ya dawo gida ya cigaba da fadada kamfanin Facebook. A shekarar 2017 jami’ar Harvard din ta kira shi ta bashi lambar girmamawa ta digiri, a inda ya rubuta a shafinsa na Facebook “Mama, na sha fada miki cewa zan koma in samo digiri ta”

Mark Zuckerberg
Darasi – Yin nasara ba sai da digiri ba.
Yin digiri ba shi ke nuna cewa kanada ilimi ba, ba kuma shi ke nuna cewa zakayi nasara ko baza kayi ba. Ilimi ya kasance ginshikin Dan Adam, amma fasaharka ta kasance abunda zata taimaka maka a ko ina.

9. Mike Adenuga
Mike Adenuga shine mutum na biyu da yafi kowa kudi a Nigeria bayan Dangote. Da sana’ar tuki yayi amfani wajen samun kudin da zai biyawa kansa kudin makaranta haka mahaifiyarsa take sayarda soft drinks a karamin shago domin ta taimaka masa wajen karatu lokacin da yake jami’ar Pace dake America. Bayan ya gama karatun nasa ne ya dawo ya cigaba da sana’ar mahaifiyarsa. A yau kamfaninsa na Glo shine na uku a kamfanonin sadarwa na Nigeria.

Mike Adenuga
Darasi – Ba ‘ya’yan attajirai bane kawai suke yin nasara.
A duniyar da muke ciki yau, idan kaga wani yana karatu a makaranta mafi kyau da karatu to fa sai ‘ya’yan masu hannu-da-shuni. Adenuga baiyi wasa da damarsa ta kasancewa direban taxi domin biyawa kansa kudin makaranta ba.

Madogara: The Opening Gates of Success – https://mohiddeenblog.blogspot.com/2017/10/the-opening-gates-of-success.html

Da fatan zamu dauki darussa ko kadan ne a dangane da rayuwar wadannan mutane, Allah yasa mu dace, Ameen.

Bissalam!

Mohiddeen Ahmad
03/05/2020

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *