0

Madogaran Nasara (4)

Cigaba…

6. Bill Gates
Mashahurin masanin na’uran nan na kasar America kuma wanda ya rike kambun wanda yafi kowa kudi duniya na sama da shekaru 5 wato Bill Gates. Bill Gates ya fara nuna soyayyarsa ga na’ura da kuma son koyonta tun yana yaro, a inda iyayensa suke son yayi karatu ya zama lauya, amma hakan bata yiwu ba. Shigarsa makaranta yafi mayarda hankali a dakin bincike na na’ura (computer lab) a inda ya hadu da Paul Allen suka fara kirkira manhajoji na na’ura har izuwa nasararsu ta gina kamfanin Microsoft. Daga karshe Bill Gates ya bar karatu sa’adda ya koma gida domin ganin Microsoft ta ginu.

Bill Gates
Darasi – Burin iyaye. 
Iyayen Bill Gates sun jajirce cewa dole sai dansu ya zama lauya, a inda basuyi tsammanin akwai wata kaddararsa da basu sani ba, sai gashi ta bayyana akan dansu.
Shawara: idan kanada ‘da kayi kokari ka fahimci me yafi mayarda hankali akai. Ko kai baka son abun, matukar dai yanada kyau to ka kasance mai bashi gwarin gwiwwa domin cimma burinsa. Nima mahaifina ba na’ura yaso na karanta ba, amma da yaga nafi mayarda hankali a wajen sai ya bani goyon baya dari-bisa-dari.

7. Aliko Dangote
Bakanon da yafi shahara a bangaren kasuwanci da kudi a yanzu shine Aliko Dangote. Dangote ya gama karatun digirinsa na farko a kasar Cairo a 1977, sannan ya dawo Nigeria a inda kakansa Alhaji Alhassan Dantata ya bashi rancen N500,000 domin yin jari. A matsayinsa na wanda yayi karatu a waje kuma yasan yadda kasuwancin wadannan kasashe yake sai ya fara shigo da shinkafa da sugar daga Thailand da Brazil a inda yake samun riba sosai a kullum. Masana sukace N500,000 a lokacin zata iya sayen mota kirar marsandi (Mercedes Benz) guda 100 a Nigeria. Bayan wata 3 Dangote ya dawo wa da kakansa kudaden da ya ranta a wajenshi a maimakon yarjejeniyarsu cewa zai dawo dasu bayan shekaru 3

Aliko Dangote
Darasi – Kasada (risk)
Ba kowane matashi bane zai karbi kudi yanzu kimanin akalla N10m sa’annan ya fara kasuwanci da su batare da ya lalata su ba. Akwai lokacin da Dangote yayi taron murnar zagayowar ranar haihuwarsa a Lagos yake cewa “Matasan yanzu bazasu iya yin acaba cikin dare suna neman kudi ba. Ina tuna lokacin da nake haka a shekarun baya ina matashi a cikin garin Lagos”

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *