0

Madogaran Nasara (3)

Cigaba…

4. Larry Ellison
Larry Ellison shine ya kirkiri kamfanin rumbun bayanai na Oracle. Shine wanda mahaifiyarsa ta kaishi raino bayan mahaifinsa ya mutu a lokacin da yake aiki a matsayin matukin jirgin saman sojojin kasar America, amma saboda talauci da rashin halin da mahaifiyarsa zata samu damar daukan nauyinsa yasa ta kai shi raino wajen wata innarta a lokacin yanada watanni 9 a duniya. Abun mamakin tun daga wannan lokaci bai sake haduwa ta ita ba sai bayan shekaru 48. A yau Ellison shine na 6 a masu kudin duniya a inda zai iya daukar nauyin marayun sama da million 10 shi kadai.

Larry Ellison
Darasi – Maraici. Maraici bai hana Ellison zama jajirtacce a fannin kasuwanci domin yin nasara ba. Bai dauka cewa dan shi maraya bane ba zai iya ba.

5. Mubarak Muyika
Masanin computer programming kuma dan kasuwa, shine CEO na kamfanin Zagace. An haifi Muyika a 1994 a Kenya kuma anan ya tashi yayi wayo. Mahaifinsa ya rasu lokacin yana da shekaru 2 a duniya, haka mahaifiyarsa ma ta rasu lokacin da ya cika shekaru 10. Muyika ya zauna a wajen makuransa (adoptive parents) a lokacin da suke da kamfanin buga littatafai. Saboda haka Muyika yayi amfani da wannan dama ya koyawa kansa yadda ake kirkira website kuma yayiwa wannan kamfani.
Tun Muyika yana dan shekaru 16 ya samar da kamfanin kirkira websites da hosting na Hype Century Technology & Investment Limited wadda ta kai shi ga nasarar samun lambar yabo ta Anzisha Prize. A yau Muyika ya zama mashahurin mutum a kasar Kenya, dudda ma kamfanoni da dama suna neman hadin gwiwwarsa a kasar America.

Mubarak Muyika
Darasi – Maraici. Hausawa sukace babu maraya sai rago. Ka kasance mai samun kwarin gwiwwa da wannan zance na bahaushe ba wai sarewa ba. Ka jajirce, ka nema kada kace wai babu mai taimaka maka.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *