0

Madogaran Nasara (2)

Cigaba…

2. WhatsApp Developers

Brian Acton da Jan Koum

Brian Acton da Jan Koum sune suka kirkiro manhajar WhatsApp a shekarar 2009. Dukkaninsu sunyi aiki a kamfanin Yahoo. Koum bayahuden kasar Ukraine ne, amma suka kauro California da zama a 1992 lokacin yana shekaru 16 shi da kakarsa. Lokacin da ya kai shekaru 18 ya fara koyon computer programming kuma ya hadu da Brian Acton bayan ya gama jami’a har ya fara aiki a kamfanin Yahoo. Abokantakarsu tayi kamari har zuwa 2007 lokacin da suka bar aiki a kamfanin Yahoo, kuma a shekarar 2009 suka kirkiri WhatsApp. A cewarsu manhajar zata kasance ta tura sakonni ne dan haka ta samo sunanta daga kalmomin “What’s up” kuma a shekarar 2014 shugaban kamfanin Facebook Mark Zuckerberg ya nuna kudirinsa na son sayan wannan kamfani a inda suka sayar masa akan kudi $19.3b. Amma kafin hakan fa dukkaninsu sun nemi aiki a kamfanin Facebook din sun fadi. Amma yanzu Koum shine Managing Director na Facebook a inda yake da shiyyar $2.4b.

Darasi – Tsammani abunda bakayi tsammani ba.
Jan Koum da Brian Acton basu taba tsammanin samun damar zama MD na Facebook ba, amma dalilin fikira da nasararsu ta kirkirar kamfanin WhatsApp, yanzu gashi hakan ya tabbata.

3. Takaddamar Yahoo da Google

Larry Page da Sergey Brin

Kasan kamfanin da ya jagoranci intanet na sama da shekaru 10? Wannan kamfani shine Yahoo! A shekarar 1996 Larry Page da Sergey Brin suka kirkiri Google search engine a matsayin research project nasu lokacin da suke matakin karatu na digirin-digirgir (PhD). Da aikinsu yayi kyau kuma masana suka shaida da haka sai sukayi kokarin sayarwa kamfanin Yahoo wannan manhaja tasu ta Google a shekarar 1998 saboda su, a fadarsu karatu suka sa a gaba, amma kamfanin Yahoo yaki sayan Google. Suka kara komawa kamfanin Yahoo domin ya sayi mahajarsu a kan kudi $5b a shekarar 2002 amma Yahoo yace yayi tsada dan haka ya fasa saya.
Kamar yadda tarihi ya nuna, Mark Zuckerberg da kansa yayiwa kamfanin Yahoo tayin sayan Facebook a shekarar 2005 akan kudi $1b amma sukace sai $850m, idan kuwa bai sayar hakan ba yayi tafiyarsa kawai. Dan haka masu kamfanin Google da Facebook suka tafi suka kafa kasuwancinsu ba tare da tunanin sayar da su ba.
A shekarar 2016 kuma kamfanin Verizon ya sayi Yahoo akan kudi $4.8b, ya fadi warwas!

Darasi – Babu wanda ya san abunda zai faru gobe.
Damar da kamfanin Yahoo suka samu kuma suka watsar ne tasa suka fadi? A’a, rashin sanin muhimmancin kasuwa da CEO nasu yayi ne ya karya kamfaninsu. A yau kamfanin Facebook da Google zasu iya sayan Yahoo sau fiye da dari ma ba tare da sun jijjiga ba. Kada kayi wasa da damarka.

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *