0

Madogaran Nasara (1)

Nasara ta kasance kishiyar faduwa. Kowa da ka gani a doron kasa yana neman hanyar nasara ne. Shahararrun mutane a fannin cigaba a duniya sunce “nasara ta kasance kishiyar faduwa da take kai mutum babban matakin da baiyi tsammani ba.” A yau mafi shahararrun mutane a duniya sun kasance yan kasuwa ne. Saboda me? Sun kasance masu kasada da rayuwarsu, gwagwarmaya, da fuskantar kowane irin kalubale domin kai su gaci.
A yau nazo muku da labaran wasu manyan shahararrun mutane a duniya da kuma yadda sukayi nasara, a hakika kowane daga cikinsu akwai darasin da zamu iya dauka a rayuwar shi.

#1 Jack Ma
Sanannen dan kasuwan nan na kasar China, shugaban kamfanin Ali Baba mai suna Jack Ma ya kasance mutumin da duniya bazata manta dashi ba domin irin gwagwarmayar da ya sha a rayuwa domin neman yayi nasara. Faduwa ta kasance babbar abokiyarsa a da, saboda;
-Ya fadi a jarrabawar shiga kwaleji sau 3
-Ya nemi shiga jami’ar Harvard sau 10 yana faduwa
-Ya nemi aiki sama da sau 30 amma bai samu ba
Wannan kadan daga cikin abubuwan da yake fada kenan. Amma nasararsa ta fara ne a lokacin da yaje kasar America a shekarar 1994 sannan ya samu ilimin intanet. Anan yayi tunanin samun damar neman kudi da shi bayan ya kirkiri shafinsa na yanar gizo na farko, anan kuma mutane da dama daga kasarsa ta China suka rinka turo masa sakonni suna so su san wanene shi, saboda sabon abu ne kirkiran shafin yanar gizo a wajensu.
Jack Ma yana ganin haka yace da abokansa tabbas dama ta samu, dan haka ya bude team dinsa mai suna China Yellow Pages suna kirkirawa mutane, kamfanoni da gwamnatoci websites suna samun kudi. A cikin shekaru 3 suka tara sama da $800,000. A yau Jack Ma shine mutumin da yafi kowa tarin dukiya a kasar China sannan daya daga cikin mafi shahararrun mutane a nahiyar Asia baki daya.

Darasi – Jarircewa.
Ba kowa bane zai iya irin faduwar da Jack Ma yayi sa’annan ya jure. Shi da kansa ya fada; lokacin da aka zo garinsu daukar ma’aikata domin kai su America su 24 ne sukaje wajen kuma aka dauki 23, shi kadai ne bai samu ba. Da ace a kasar Hausa ne da sai ace ai asiri akai masa ya kasa samun aiki shi kadai. Jack Ma ya kasance gwarzo wanda ya jajirce akan yin abunda ya sa a gaba. Shiyasa ake cewa “Jajircewa hanyar nasara ce”

Mohiddeen Ahmad

I am Muhammad Auwal Ahmad (Mohiddeen), a technologist and a writer. I Specifically write on sciences and modern technology. Hit my about page to learn more about me.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *