Mars

Credit: ESA

Duniyar ta kasance ta huɗu a jadawali kuma wacce ake tunanin rayuwa za ta iya kasantuwa a cikinta. Ita ce duniyar da ke kama da duniyar Earth, sai dai ba ta kai Earth girma ba.

Bayani

Nauyi: kaso 15% na duniyar Earth

Faɗi: 6,779 km

Yanayi: 26.6 °C (80 °F)

Watanni: 2

Ƙarfin Maganaɗiso: 3.71 m/s^2

Tazarar da ke tsakaninta da rana: kilomita miliyan 227.9

Ƙarin Bayani

Yadda duniyar Mars take. Photo credit: NASA

Duniyar Mars tana da launin ja, sannan tana da watanni biyu; Deimos da Phobos. Ana yawan tura jirage duniyar Mars don gudanar da bincike, saboda ita ce duniyar da ta fi dacewa da rayuwa bayan duniyar Earth. A shekarar 1976 jiragen Viking 1 da Viking 2 suka dira a duniyar Mars, haka nan a shekarar 2003 da 2012.

Madogara

[1] Astronomy > Mars > References